Shahararriyar jarumar nan ta shirya fina-finan Hausa, Hadiza
Aliyu Gabon na shirin kwancewa wasu mutane dake rike da kudinta zani a kasuwa.
Bisa ga sakonnin da jarumar ta fitar, tace duk wani mai rike
da kudin ta ya shirya fuskantar fushin ta idan baiyi gaggawa biyan bashin da
take bin sa ba. Jarumar ta kai makura kuma kamar yadda ta sanar bata son jin
wani labari, kudinta kawai take bukata kuma idan ba'ayi hakan ba zata fallasa
sunayen masu.
Gabon tace bata bukatar wadanda take bi bashi su kira ta ko
su tura mata sakon. Iya sakon da take son ta gani daga gare su shine alamar an
tura mata kudinta. Cikin kudin ta dake hannun jama'a akwai miliyan N2.8, dubu
N350, dubu 75 da kuma dubu N30.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku