AN KARA YAWAN 'YAN SANDA A JIHAR PLATEAU DOMIN KAWO KARSHEN TARZOMA



Hukumar ‘yan sanda ta kara tura yan sanda masu kwantar da tarzoma zuwa jihar Plateau inda ake rikicin kare dangi, wanda mataimakin shugaban hukumar ‘yan sanda ta kasa ya jagoranta domin kawo zaman lafiya a yankin Riyom, Barikin Ladi da kuma Jos ta kudu.
Tuni aka kai jirage masu saukan angulu guda biyu, Motoci masu dibar mayaka guda biyar, Hukumar yan sanda CTU masu kwantar da tarzoma, da kuma yan sanda masu sa fararen kaya.
Cikin wadanda aka tura sun hada da hukumomin ‘yan sanda masu bincike da hukunta masu laifufuka wato FCIID da kuma masu tarwatsa  da kuma lalata wadansu na’ura masu fashewa kamar su bam. EOD, Jami’an ‘yan sanda masu amfani da karnuka domin gano masu laifi (K9) da kuma ‘yan sanda masu yaki da ‘yan fashi SARS.
Rahotanni sun nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alwashi cewa gwamnatinsa ba za ta huta ba har sai an gano masu kisan da masu goyon bayan aikata laifin.
Mista Terna Tyopev, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Plateau ya ce an kashe mutane 86 ne yayin da mutane shida suka jikkata.
Wadannan hare-haren sun kasance a garuruwa 11 a gundumar Gashish a Barkin Ladi LGA da kuma wasu al'ummomin da ke Bokkos da suka fara ranar Juma'a.
Don haka, hukumar ‘yan sanda tana sanar da jama’a cewa idan sun sami labarin tashin hankali, harbe-harbe, ko kasha – kasha a yankunan, sai su kira wadannan lambobin wayar: 07059473022, 08038907662, 08075391844, and 09053872296’' domin daukar mataki nan take.


Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta


Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments