CUTAR EBOLA TA YADU ZUWA WASU MANYAN BIRANEN CONGO

Ministan kiwon lafiyar kasar Congo ya ce cutar Ebola ta yadu zuwa babban birnin kasar Equateur, batun da ya jawa tashin hankali a kasar baki daya.
Ministan kiwon lafiya, Oly Ilunga, ya ce mutane biyu da ake zaton sun kamu da cutar zazzabin sun ruwaito wa yankunan kiwon lafiya na Wangata, wanda ya hada da garin Mbandaka, kimanin kilomita 150 (93 mil) daga Pleasero, wata karkara inda aka samu barkewan cutar.


Yace wani samfurin ya tabbatar da cutar Ebola, ya kawo adadin marasa lafiya a yankuna uku.
Ilunga ya ce kasar Congo tana fuskantar barazana da kuma babban hatsari, sakamakon yaduwar cutar. Ya ce masana ilmin lissafi suna aiki tukuru don gano adadin yawan wadanda suka kamu da cutar, ciki har da mutane 500 da aka gano.
Kasar Congo ta bayar da rahoton cewa mutane 23 ne cikin 42 da suka rasa ransu sakamakon barkewan cutar a cikin kasar.

Comments