ABIN DA YA KAMATA KO WANNE MUSULMI YA SANI GAME DA AZUMIN WATAN RAMADAN

1- menene watan Ramadan?
Allah madaukaki Yana cewa a cikin suratu yunus, ayah ta biyar: {Shine Wanda Ya sanya muku rana babban haske, da wata mai haske, kuma Ya kaddara shi manziloli, domin ku san kidayar shekaru da lissafi. Allah bai halitta wannan ba face da gaskiya, yana bayyana ayoyi daki–daki domin mutane wadanda suke sani}.

Allah Shine Ya halicci wata domin mu san yaushe kwanan wata yake farawa kuma yaushe yake karewa, wannan kwa ta hanyar ganinsa; domin wata ko yayi kwana ishrin da tara ko kuma yayi talatin, ba yanda za'a yi ya ka'sa ga ishrin da tara, ko kuma ya kara akan talatin.
Wannan kwa sune ake kira watannin muslunci guda goma sha biyu, wadanda sune kamar haka:
1- muharram
2- safar
3- rabi'ul awwal
4- rabi'us sa'ni
5- jumadal u'la
6- jumadas saniya
7- rajab
8- sha'aban
9- ramadan
10- shawwal
11- zul ki'idah
12- zul hijjah
Za mu ga cewa a cikin wadannan watanni akwai wanda ake kira (Ramadan), shine wata na tara.

2- muhimmancin watan Ramadan, da kuma wajabcin azumtar shi
- A cikin watan Ramadana ne ayo'yi na farko na Alkur'ani suka sauka, Allah madaukaki Yana cewa: {watan ramalana ne wanda aka saukar da Alkur'ani a cikin say a shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi}kuma kamar yanda yake a bayyane a cikin a'yar, Allah Ya umarci bayinSa muminai da azumtar watan gaba dayansa; domin su godewa ni'imarSa ta saukarda wannan Alkur'ani wanda a cikinSa ne shiriyar bayi take da dadin kan su.
Idan namiji ya balaga; ma'ana ya kammala shekara goma sha biyar, ko gashin ma'ra ya toho masa, ko maniyi ya sauko masa; to a wannan lokacin wajibi ne akan sa ya azumci watan Ramadana wanda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) Ya gaya mana muhimmancinsa  ta hanyar sanya shi cikin ginshikan muslunci biyar.
Wajibi ne akan musulmi baligi ya azumci watan Ramadan gaba daya; domin ya samu ladan wannan azumi, kuma ya tsira daga ukubar Ubangiji akan wanda bai yi azumi ba, ba tare da uzuri ba.
- Wanda kwa bai balaga ba, azumi bai zan wajibi akan sa ba, duk da ke ya kamata majibintan al amarinsa su horar da shi a kan azumin, domin yayin da suka balaga su kasance ba su da matsala game da azumin.

3- kaka ake azumtar watan Ramadana
Ma'anar azumi shine: niyar azumtar watan ramadan gaba daya; ta hanyar nisantar ababenda ke karya azumi, wadanda asalin su uku ne:
1- kar ka ci kome, ka nisanci duk abinda ake kira abinci ko yake da ma'anar abinci tamkar Karin ruwa na likita da abinda yayi kama da haka, amma ababen da ba su da ma'anar abinci halal ne; kamar kwali, da asuwaki, da makilin na wanke hakora, da turare da abinda yayi kama da haka.
2 – kar ka sha kome; ka nisanci duk abinda ake kira abinsha ko yake daukar ma'anarsa; misali: shan sigari da abinda yayi kama da haka. Amma ababenda ba su da ma'anar abinsha wadannan halal ne ba su da laifi; misali yin wanka, ko sanya maganin kunne ko ido, ko hada yawu, da abinda yayi kama da haka.
3 – kar ka tara da matar ka; ka nisanci duk abinda zai fitar maka da sha'awarka,tare da cewa sumbatar iyali da rungumarta ba ya karya azumi, duk dake nisantar shi shine ya kamata, musamman ga wanda ba ya iya mallakar kan sa.
Kuma futar da maniyyi a halin bacci ba ya karya azumi domin ba da niya ya futo ba.

4- Abin buda baki
Abinda mai azumi yake buda baki da shi, shi ake kira "ifdar".-
- Kuma abinda yafi shine a gaggauta buda baki; a yishi da zaran rana ta fadi ba tare da jinkirta shi ba har zuwa lokacin isha'i ba.
- kuma ya halitta ga mai azumi ya buda baki da ko wane abinci ko abin sha, duk dake abinda ya fi shine ya buda baki da danyan dabino (maga), idan bai same shi ba, ya buda baki da ruwa.
- ya kamata mai azumi ya lazamci ladubban ci da sha, wadanda mafi muhimmaci a cikinsu sune:
1- ya ce: bismillah (zan sha, ko zan ci da sunan Allah).
2- ya ci da dama.
3- ya ci gaban sa.
Idan kuma mai azumi ya so sai ya karanta daya daga addu'o'i da suka inganta; kamar : (zahabaz zama'a, wabtallatil uru'k, wa sabatal ajru in sha' Allah); ma'ana: kishirwa ta tafi, kuma jijiyoyi sun jiku, sa'annan lada ya tabbata da ikon Allah.

5- abincin sahur
-abincin da mai azumi yake ci gabanin asuba shi ake kira sahur.
-kuma abinda ya fi shine jinkirtar da shi har zuwa kusan ketowar alfijr, kuma abinci ne mai anfani; domin ya bada karfin gyuwa wajen azumtar yini da ke biyowa.
- ya kamata mai azumi ya lazamci ladubban ci da sha lokacin sahur kin sa, wadanda mafi muhimmaci a cikinsu sune:
1- ya ce: bismillah (zan sha, ko zan ci da sunan Allah).
2- ya ci da dama.
3- ya ci gaban sa.

6- ababen da ya kamata mai azumi ya aikata cikin azumin sa
Idan mai azumi ya samu damar tafiyar da lokacin sa a cikin da'a ga Ubangiji wannan shine ya fi; kamar karatun Alkur'ani da tafsirinSa, ko sallah da ambaton Allah, da sadaka, da kyakyawar magaana, da dabi'u kyawawa, kuma ya yawaita adu'a har buda baki.
Ibn Abbas (Allah kara yarda da shi) ya ruwaito cewa: manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) Shine ma fi karamcin mutane, kuma Ya fi karamci a ramadan lokacin da Mala'ika Jibril Yake haduwa da Shi, Ya kasance yana haduwa da Shi a cikin kowane dare na ramadan; lalle karamcin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) wajen raba alkhairi ya fi iska da aka saki.
Kuma bayan ya buda baki ya kamata ya sallaci sallar asham tare da musulmi dan rabbanta da lada mai yawa a cikin yini da daren sa.

7- ababen da bai kamata mai azumi ya aikata ba  cikin azumin sa
- idan musulmi ya kasance a halin azumi yana wajabta akan sa ya nisanci ababen ki da haramun; ya guji fasikanci da yasashen zance, kuma kar ya daga muryar sa akan abokin maganar sa, ko da an masa kuskure. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) Yana cewa kamar yanda bukhari ya ruwaito: "wanda bai bar Magana da aikin zur ba; Allah ba Ya bukatar ya bar abin ci da shan shi". Kuma manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) Yana cewa: "azumi garkuwa ne; kar mai azumi ya kusanci mace, kuma ya nisanci duk jahilci, idan wani ya tsokane shi, ko ya zage shi yace: ni azumi ni ke". Bukhari ya ruwaito shi.

8- uzurin da ke bada damar a ajiye azumi a ramadan, kuma kaka ake biyan azumin da aka sha
- idan mai azumi ya manta ya ci ko ya sha sai ya ci gaba da azumin sa; saboda mantuwa  uzuri ne da shari'a ta yarda da shi; dan haka ba zai rama ba bayan ramadan.
- haka ma idan ya ci ko ya sha da jahilci sai ya ci gaba da azuminsa idan jahilcin sa ya gushe; domin jahilci uzuri ne a cikin shari'ar muslunci; wannan kwa shin ya jahilci wajabcin azumtar watan ne, ko ya jahilci shigar lokacin ne ko hutar sa; kuma ba zai rama ba.
- haka ne wanda aka tilasar akan ci ko shan wani abu ya ci gaba da azumin sa, saboda tilasarwa uzuri ne da shari'a ta yarda da shi; kuma ba zai rama wannan yinin ba bayan watan ramadan. Haka ne ma game da wanda yayi mafarki sai maniyi ya zo masa, azumin sa ya inganta, kawai abinda zai yi shine wanka.
Idan kuma musulmi ya kasance a cikin halin balaguro, kuma ya ga zai iya ci gaba da azumin sa ba tare da takura ba sai ya ci gaba da azumin sa; saboda shan azumi a halin balaguro sauki ne da Allah Ya bada; Yana iya ya bar azumi kamar yanda yake iya ya yi azumi; sai ya zabi ma fi sauki a gare shi.
- haka ne ga wanda baya da lafiya kuma ba ya iya yin azumi; yana da damar ya sha, idan watan ya kare sai ya rama kwanakin da ya sha na ramadan. Misali: idan ya sha kwana goma sai ya rama kwana goma bayan ramadan tsakanin shawal da sha'aban.
- sa'annan duk abinda yayi kama da rishin lafiya yana daukar hukuncin rishin lafiya; kamar  yin kaho ko bada jini wanda ke raunana jiki.
- mace mai ganin jinin al'ada haram ne tayi azumi; zata sha ruwa kuma ta rama kwanakin da ta sha bayan ramadan.
- haka ne mace mai jego ma hukuncin ta kamar hukuncin mai ganin jinin al'ada ne.
- Amma gajiyayyen da ba ya iya yin azumi ko wanda likitoci suka tabbatar  cewa ba ya iya yin azumin; wajibi ne akan sa ya ciyar da miskini guda abinda zai ishe shi madadin ko wane yini; kenan zai ciyar da miskini ishrin da tara ko talatin.

9- idan watan ramadan ya kare sai idin musulmi
- idan musulmi suka azumci watan ramadan, rana ta farko a cikin shawal rana ce ta idin azumi; a cikin wannan ranar suna farin ciki saboda sun samu damar azumtar wannan wata, kuma suna nuna farin cikin su ta hanyoyi kamar haka:
1- suna nuna farin cikin su ta hanyar godewa Allah da Ya shar'anta wannan iba'da.
2- kuma suna nuna farin cikin su ta hanyar yawaita kabbara, suna masu maimaita: "Allahu akbar, Allahu akbar, la' ilaha illa lah, Allahu akbar, Allahu akbar, wa lillahil hamd".
3- suna kuma nuna murnar su ta hanyar sallar idi bayan hutowar rana da lokaci kadan; inda suke sallatar raka'a biyu a cikin jama'a, suna ma su sanya sabbin kaya ma su suturcewa.
Dukkan wadannan ababe suna karfafa mana cewa farin cikin musulmi babu shaye shaye ko wauta ko fajirci a ciki kamar yanda yake a wajen wasu al'ummomi, hasali ma na musulmi ladabi, da godiya, da sadaka, da so da kauna, da sadar da zumunta, da afuwa, da dukkan alkhairi ke ciki.
Sama da haka shi musulmi yana jiran babban idi ne ranar kiya'ma yayin da za su shiga Aljanna inda za su dawwama har abada; su ci, su sha, suna matasa; ba tsufa, ba ciwo, ba tabewa, wannan kwa shine babban rabo.
Wannan kuma shi ya sa musulmi yake rayuwa cikin nutsuwa duk halin da yake ciki; duk yanda musiba ta same shi ya san da cewa abinda Allah Ya tanadar masa ya fi wannan musibar, {kuma abin da aka ba'su daga kome, to, jin dadin rayuwar duniya ne da kawatarwa. Kuma abin da ke wurin Allah, shine mafi alheri, kuma ma fi wanzuwa} suratul kasas, aya ta 60.      

Comments